An yi kan-kan-kan a zaben Senegal

Image caption 'Yan takarar shugabancin kasar Senegal

Sakamakon da ba a tabbatar da sahihancinsa ba na zaben shugaban kasar Senegal mai cike da takaddama ya nuna cewa babu tazara mai yawa tsakanin Shugaba mai ci Abdoulaye Wade da babban mai adawa da shi, Macky Sall, wanda ya taba rike mukamin Firayim Minista.

Idan ba a samu dan takarar da ya yi rinjaye ba, to wajibi ne a tafi zagaye na biyu a zaben.

Shugaba Wade dai mai shekaru tamanin da biyar a duniya na neman darewa kujerar shugabancin kasar a karo na uku duk da cewa kundin tsarin mulki ya tanadi wa'adi biyu ne kawai.

Shawararsa ta sake tsayawar kuma ta haddasa tarzoma a kasar; yayin da ya je kada tasa kuri'a ma har ihu wadansu mutane suka yi masa suna cewa kauce dattijo.

An dai gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Karin bayani