Amurka na ji-ji-da-kai, in ji China

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Firayim Ministan China, Wen Jibao

Wani sharhi da jaridar Jam'iyyar Kwaminisanci ta China ta wallafa ya ce bayan abin da ya faru a Iraki, Amurka ba ta da sauran hurumin yin magana da yawun kasashen Larabawa.

Sharhin dai na zuwa ne bayan kakkausar sukar da Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, ta yi cewa kujerar na-kin da China da Rasha suka hau dangane da wani kudurin Majalisar Dinkin Duniya a kan Syria abin kunya ne.

Ita dai China ta yi amanna cewa ya kamata a kyale Shugaba Bashar al-Assad ya aiwatar da sauye-sauyen da za su kawo karshen zubar da jinin da ake yi.

A al'adance China ba ta tsoma bakinta a harkokin cikin gidan wadansu kasashen.

Sai dai kasashen duniya na matsa lamba akan ta da kuma Rasha domin su goyi bayan daukar mataki a kan Syria.

Rikicin Syria zai kankane taro a Geneva

Ana sa ran tashe-tashen hankulan da ake ci gaba da samu a kasar ta Syria za su kankane ajandar taro na baya-bayan nan na hukumar kiyaye hakkokin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya wanda za a fara a Geneva.

Mai yiwuwa mambobin hukumar su yi kira da a tsagaita wuta, sannan kuma a baiwa kungiyoyin agaji irinsu Red Cross dama su gudanar da ayyukansu a kasar.

Ga alamu kasashe mambobin hukumar za su doge wajen matsa lamba, ba kawai a kan Syria ba, har ma da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya gaza cimma matsaya a kan yadda za a bullowa rikicin.

Karin bayani