Sojin Najeriya sun gargadi masu bin ayarin motocin hukuma

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

Sojin Najeriya sun gargadi masu motar da kan bi ayarin motocin jami'an gwamnati da ke da ikon wucewa shingayen tsaro kai tsayej domin su ma su samu su wuce ba tare da an duba su ba.

Suka ce duk abin da ya samu wanda ya yi hakan shi ya ja wa kansa.

A wani lamarin da ya shafi tsaro, dazu ne da rana 'yansanda suka bude wuta a kan wata karamar mota kirar Golf, wadda aka ce ta haya ce wadda ke dauke da wasu mutane biyar a ciki, bayan da direban motar ta kutsa wani shingen da aka hana bababen hawa wucewa a Dutse babban birnin jihar Jigawa.

Mutane ukku daga cikinsu wadanda suka hada da direban ne harbin ya sama, kuma a halin yanzu suna can a kwance a asibiti karkashin kulawar yan sanda.

Su kuwa hukumomin tsaro a jihar Bauchin Najeriya sun yi karin haske ne a kan hare-haren bamabamai da kuma bindigogin da aka kai jiya da dare a garin Jama'are.

Jami'an tsaron suka ce dan sanda daya ne ya rasa ransa,sannan wani jami'in tsaron kuma ya samu rauni.

Haka kuma ofishin 'yansandan da kuma bankin da aka kai wa harin sun yi kaca-kaca.

Maharan dai sun yi wa wuraren biyu dirar mikiya ne.

A jihar Filato mai makwabtaka da jihar ta Bauchi kuma, hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa mutumin da aka lakada wa duka har ya mutu bayan tashin bam din wani harin kunar bakin wake a majami'ar COCCIN ranar Lahadi, mamba ne a majami'ar.

Karin bayani