Jirgin ruwan Italiya na cikin tsaka-mai-wuya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jirgin ruwan Italiya

Wani katafaren jirgin ruwan Italiya da ke dauke da fiye da mutane dubu yana can yana tangal-tangal a wani bangare na Tekun India inda 'yan fashin teku na Somalia suke cin karensu ba babbaka.

Ma'aikatan jirgin mai suna Costa Allegra sun aike da sakon neman daukin gaggawa ne bayan gobara ta tashi a daya daga cikin injinan da ke samar da wuta ga jirgin.

Kamfanin da ya mallaki jirgin ruwan na Costa Allegra shi ne kuma ya mallaki jirgin ruwan nan Costa Concordia, wanda ya yi hatsarin da ya hallaka mutane da dama.

Karin bayani