An cire tantunan da masu bore suka kafa a London

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana cire tantunan da masu bore suka kafa a London

Wasu jami'ai da ke aiwatar da umarnin kotu sun kawar da dukkan tantunan da wasu masu bore suka kafa a gaban majami'ar St. Paul da ke birnin London.

An dai kawar da tantunan masu boren ne cikin ruwan sanyi duk da cewa wasu masu boren sun yi kokarin sake kafa tantunan nasu nan take.

Masu boren dai sun fusata, wasu daga cikinsu ma sun yi ta yiwa 'yan sanda kalamai masu zafi.

Suna dai yin boren ne domin nuna rashin amincewa da tsarin tattalin arziki da ke fifita masu hannu da shuni.