An watsar da tokar gawarwakin mutanen da suka mutu a Amurka

Hakkin mallakar hoto DOUG KANTERAFPGetty Images
Image caption Daya daga cikin wuraren da suka rushe a lokacin harin da aka kai a Amurka

Wani bincike ya gano cewa an zubar da tokar gawarwakin wasu daga cikin mutanen da suka rasa rayukansu a harin sha daya ga watan Satumba na 2001 a Amurka a wadansu ramukan zubar da shara.

Tokar ta wadansu sassan gawarwakin mutanen da suka rasa rayukasnu ne a ma'aikatar tsaron Amurkar ta Pentagon da kuma jirgin saman da aka yi fashinsa wanda ya fadi a Pensylvania a ranar.

Gawarwakin, wadanda aka danka alhakinsu a hannun wani dakin ajiyar gawarwaki a sansanin sojin sama na Dover, na mutanen da aka kasa gano ko su waye su ne.

Janar John Abizaid mai ritaya, wanda ya jagoranci wani bincike da Pentagon da gudanar a kan al'amarin, ya ce bai kamata a zubar da tokar a ramukan ba.

Karin bayani