Romney ya ba da mamaki a zaben fidda gwani

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mitt Romney

Mutumin da ke kan gaba a neman tsayawa takarar shugabancin Amurka a jam'iyyar Republican, Mitt Romney, ya lashe zaben fidda gwanin da aka gudanar a jihar Michigan.

Mitt Romney, ya kuma lashe zaben fidda gwanin da aka gudanar a jihar Arizona, lamarin da ya sanya shi da magoya bayansa ke ta shagulgula.

Nasarar da ya yi a Arizona ta zo da sauki fiye da yadda aka zata, amma masu sharhi na ganin nasarar da ya yi a Michigan ta fi muhimmanci.

A Michigan din dai ya fuskanci zazzafan kalubale daga Rick Santorum, wanda kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa zai iya kayar da Mista Romney.

Mista Romney ya shaidawa magoya bayansa cewa nasarar tasa tana da muhimmanci matuka:

''Na gode Arizona, wannan babbar nasara ce a Arizona a yau; sannan na gode Michigan, madalla da wannan nasara. Wannan babbar rana ce''.

Yanzu dai za a jira zuwa ranar Talatar makon gobe don ganin wanda zai samu nasara a zaben da jihohi goma za su gudanar .

Karin bayani