Syria ta ce sai taga bayan 'yan adawa

Mayakan 'yan adawar Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mayakan 'yan adawar Syria

An bayar da rahoton cewar dakarun Gwamnatin Syria sun yi kokarin dannawa zuwa Unguwar Baba Amr a Homs yayinda suke yin luguden wutarsu mafi tsanani kawo yanzu a kan Unguwar.

Jami'an Gwamnati sun ce za su kawar da mayakan yan adawa a cikin yan sa'o'i.

To amma masu fafutika sunce kawo yanzu mayakan yantar da Syria sun dakile dannawar da sojin ke yi.

Mazauna Homs sun saka neman taimako ta internet.

Da yake magana da BBC wani mai fafutika a Homs din ya ce, a yau sun wayi gari da munanan hare hare da ruwan harsasai.

A Homs, galibin luguden wutar ana yin sa ne a Baba Amr.

Hakan ya zo ne yayinda gwamnatin Syria ta ki bayar da izini ga Shugabar hukumar ba da agaji ta MDD, Baroness Valerie Amos, na shiga kasar.

Karin bayani