EU na Shirin Tallafawa Sahel da Tsaro

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Piraministan Faransa, Nicolas serkozy

Kungiyar Tarayyar Turai wato EU, na shirin aikewa da kwararrun jami'ai da za su dafa wa gwamnatin kasar Nijar dangane da kokarin da take yi na yaki da ta'addanci.

Shirin na inganta tsaron zai tunkari matsalar kungiyar Alka'ida da sauran kungiyoyin ta'addanci da ma na yan tawaye dake kokarin kawo cikas a yankin Sahel, tun bayan rugujewar gwamnatin Gaddafi.

Ministocin harkokin wajen kasashen Turai za su tattauna a kan wannan maganar cikin wannan watan.

Idan har suka amince da shirin kuma, kwararrun jami'an za su kasance a Kasar ta Nijar ne watanni masu zuwa, domin aikin horar da jami'an tsaron Kasar.

Abunda ya ja hankalin Kasashen Nahiyar turan shine awan gaba da garkuwa da Turawa da yan kungiyar Almagareb keyi abunda suka ce na bara zana garesu.

Kwararru a harkokin tsaro na cewa akwai bukatar Kasashen Duniya su taimakawa Yankin sahel kan matsalar tsaro da suke fama da shi.

EU dai tayi Amanna zata turo da tawaga zuwa Nijar musammam ma da kasar Faransa ce a kan gaba, saboda dadaddiyar hurda dan take da ita da Yankin Sahel din.

Karin bayani