'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda hudu a Bayelsa

Shugaban yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto Aliyu
Image caption Jami'an tsaro a Najeriya na fuskantar babban kalubale a gabansu

A Najeriya wasu 'yan bindiga sun hallaka 'yan sanda hudu masu sintiri a wani yankin ruwa na jihar Bayelsa da ke yankin Niger Delta mai arzikin man fetur.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da rana kuma rundunar 'yan sandan jihar ta ce tana kokarin gano mutanen da suka yi aika-aikar.

Jihar Bayelsa inda nan ne mahaifar shugaban kasar Goodluck Jonathan a baya ta fuskanci kalubalen tsaro da ke alakanta wa da 'yan gwagwarmayar yankin Niger Delta.

Kuma wannan lamarin na yanzu na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula a wasu sassan kasar.

Yawancin rikice-rikicen dai ana alakanta su ne da kungiyar Boko Haram wacce ke fada da hukumomin kasar.

Karin bayani