BBC navigation

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda hudu a Bayelsa

An sabunta: 1 ga Maris, 2012 - An wallafa a 20:39 GMT
Shugaban yan sandan Najeriya

Jami'an tsaro a Najeriya na fuskantar babban kalubale a gabansu

A Najeriya wasu 'yan bindiga sun hallaka 'yan sanda hudu masu sintiri a wani yankin ruwa na jihar Bayelsa da ke yankin Niger Delta mai arzikin man fetur.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da rana kuma rundunar 'yan sandan jihar ta ce tana kokarin gano mutanen da suka yi aika-aikar.

Jihar Bayelsa inda nan ne mahaifar shugaban kasar Goodluck Jonathan a baya ta fuskanci kalubalen tsaro da ke alakanta wa da 'yan gwagwarmayar yankin Niger Delta.

Kuma wannan lamarin na yanzu na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula a wasu sassan kasar.

Yawancin rikice-rikicen dai ana alakanta su ne da kungiyar Boko Haram wacce ke fada da hukumomin kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.