Atisayen soji a tekun atalantika

'Yan fashi teku a Somalia Hakkin mallakar hoto crown
Image caption Za a gudanar da atisayen soji domin magance matsalar masu fashin jiragen ruwa a Afirka

Rundunonin Sojin ruwa daga wasu Kasashen Afrika, za su fara wani atisaye, a tekun Atalantika da ke kudancin Najeriya.

Ana dai gudanar da atisayen ne, na hadin gwiwa, da Kasar Amurka, don neman magance barazanar kai hare- hare kan Jiragen ruwa, wanda ake ganin ya fara addabar yankin na Afrika.

Atisayen dai wanda ake wa lakabi da suna OBANGAME, zai hada da kaiwa da komowar manyan jiragen ruwa na yaki, da kuma masu saukar ungulu.

A gobe ne dai ake sa ran za a kammala atisayen.

Rahotanni na nuna cewa, harkar fashin jiragen ruwa, da kuma satar danyen mai, na karuwa a yankin tsakiya da kuma yammancin Afrika.

Karin bayani