BBC navigation

Sabon tsarin adana bayanai na Google

An sabunta: 1 ga Maris, 2012 - An wallafa a 16:33 GMT
Sabon tsarin adana bayanai na Google

An dade na cece-kuce kan wannan shirin na Google

Kamfanin matambayi baya bata na Google ya fara aiwatar da sabon shirinsa na hade taskar bayanan masu amfani da shufukansa wuri guda, duk da damuwar da Tarayyar Turai ta nuna.

Sauye-sauyen na nufin bayanan da Google ya samu na mutane zai iya mika su ga sauran shafukansa da suka hada da You Tube, Gmail da Blogger.

Google ya ce wannan tsari zai taimaka masa wurin samar da bayanai ga masu bincike.

Amma hukumomin kula da kare sirrin jama'a a Faransa sun nuna shakku kan halarcin matakin na Google ta fuskar shari'a, sannan suka kaddamar da bincike a Turai baki daya.

Google ya hade ka'idoji 60 wuri guda domin amfanin shafukansa baki daya.

Wannan na nufin tarihin yadda mutum yake neman bayani a internet wanda ake samu lokacin da mutum ya shiga shafin Google, za a iya rarraba shi zuwa sauran shafukan.

Fita daga shafin Google na rage adadin bayanan da shafin ya ajiye, sai dai - kamar sauran shafuka - Google na ajiye bayanan mutanen da bai sani ba.

'Babu abinda zai sauya'

Hukumar kula da kare sirrin jama'a ta Faransa CNIL ta aikewa Google wasika a farkon makon nan, tana neman kamfanin da ya "dakatar" da shirin.

Sai dai a martanin da ya mayar, lauyan Google Peter Fleischer ya ce a shirye yake ya amsa duk wani korafi da CNIL ke da shi.

"Kamar yadda muka fada a makon da ya gabata, duk da cewa manufarmu ta adana bayanai za ta sauya daga 1 ga watan Maris, amma muhimmacin da muke bayarwa wurin kare bayanan jama'a na nan kamar yadda yake," a cewar Mr Fleischer.

Kamfanin ya yi watsi da bukatar CNIL ta dakatar da sauye-sauyen.

Za a mayar da bayanan jama'a zuwa wannan taska daya tilo da misalin karfe 12 na daren 1 ga watan Maris.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.