Jam'iyyar ANC ta kori Julius Malema

Julius Malema Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jam'iyyar ANC a Afirka ta Kudu ta sallami Julius Malema

An kori Julius Malema, shugaban matasa na jam'iyyar ANC mai mulki a Afrika ta Kudu .

Kwamitin ladabtarwa ne na jam'iyyar ya yanke masa hukuncin mai tsauri, fiye da hukuncin dakatarwar da aka yi masa na tsawon shekaru biyar da yai ta neman a yi masa afuwa.

Wakilan kwamitin sun amince da wani hukunci ne da aka yanke masa tun a bara, wanda ya yi nunin cewa ya kawo rarrabuwar kawuna tsakanin 'ya'yan jam'iyyar.

Daga cikin kalaman da ya yi masu rikitarwa har da kiran da ya yi na neman a hambaradda gwamnati a makwabciyar Kasar Botswana da kuma maye-gurbin Shugaban jam'iyyar ANC mai ci yanzu Shugaba Jacob Zuma.

Karin bayani