Red Cross za ta shiga unguwar Baba Amr

Red Cross za ta shiga unguwar Baba Amr Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kwamitin sulhu ya nemi a bada izinin shigar da kayan agaji

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce za ta shiga unguwar Baba Amr da ke birnin Homs na Syria inda ake fama da rikici, bayan da ta samu izini daga gwamnatin Syriar.

Red Cross ta ce an shaida mata cewa za ta iya kai kayan abinci da magunguna da kuma debe wadanda suka ji raunuka.

Hicham Hassan, shi ne mai magana da yawun Red Cross a birnin Geneva kuma ya ce:

"Kungiyar Red Cross da kuma Red Crescent ta Syria, mun samu izini daga hukumomin Syria na shiga Baba Amr, amma hakan zai faru ne a ranar Juma'a".

Kwamitin sulhu ya dau matsaya

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ce wajibi ne abayar da damar shiga da kayan agaji zuwa kasar ta Syria ba tare da bata lokaci ba.

Kasashen Rasha da China sun goyi bayan kudurin duk da adawar da suka nuna a baya, kan daukar mataki kan kasar ta Syria.

Wakilin BBC a Majalisar ya ce wannan ya haifar da kwarin gwiwar cewa, mai yiwuwa su goyi bayan yunkurin da ake yi na kawo karshen rikicin.

Kwamitin ya kuma bayyana rashin jin dadinsa kan yadda aka hana shugabar hukumar kula da ayyukan jinkai ta Majalaisar Valerie Amos, izinin shiga Syriar duk da cewa an nemi hakan ba sau dayaba-ba sau biyu ba.

Dakarun adawa sun janye

Mayakan yan adawa na Syria da ke gundumar Baba Amr da aka yiwa kawanyar tsawon makonni a birnin Homs, sun ce suna janyewa bisa dalilai dabarun yaki.

Wata sanarwa da aka fitar a wani shafi na Internet da sunan mayakan 'yan tawayen Syria a birnin Homs ta ce sun dauki matakin janyewa bisa dabaru irin na yaki.

Sanarwar wadda ta ce ta fito ne daga bataliyar Baba Amr - ta ce mayakan suna janyewa ne saboda la'akari da cewar har yanzu akwai farar hula a yankin.

Sanarwar ta kara da cewa mayakan basu da isassun makamai na kare fararen hullar.

Tun farko dai wani mai fafutuka da ke cikin birnin na Homs ya ce an yiwa birnin kawanya.

Karin bayani