Mayakan adawa a Syria sun janye daga Homs

Mayakan Yan adawa a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mayakan Yan adawa a Syria

Mayakan yan adawa na Syria da ke gundumar Baba Amr da aka yiwa kawanyar tsawon makonni a birnin Homs, sun ce suna janyewa bisa dalilai dabarun yaki.

Wata sanarwa da aka fitar a wani shafi na Internet da sunan mayakan 'yan tawayen Syria a birnin Homs ta ce sun dauki matakin janyewa bisa dabaru irin na yaki.

Sanarwar wadda ta ce ta fito ne daga balaliyar Baba Amr - ta ce mayakan suna janyewa ne saboda la'akari da cewar har yanzu akwai farar hula a yankin.

Ta ce mayakan basu da isassun makamai na kare fararen hullar.

Tun farko dai wani mai fafutuka da ke cikin birnin na Homs ya ce an yiwa birnin kawanya.

Yace tun daga jiya aka katse wutar lantarki ga baki dayan birnin. haka nan shima ruwa an dakatar da shi.

Ya kara da cewar damuwar ita ce yadda mutane za su iya rayuwa, bayan irin harbe-harben da ake yi.

Ya ce ba su da abinci babu magunguna, ga kuma mutane fiye da dubu da dari hudu da suka samu raunika.

Karin bayani