Amurka ta yi wa 'yan Kasar ta kashedi zuwa Najeriya

Sakatariyar kula da harkokin Kasashen wajen Amurka Hillary Clinton Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amurka ta ja kunnen 'yan Kasar ta da kai ziyara Najeriya

Amurka ta yi wa 'yan Kasar ta kashedin cewar su kiyayi zuwa Najeriya sakamakon zargin tabarbarewar harkar tsaro a Kasar.

Ofishin kula da harkokin wajen Kasar ne ya aike wa 'yan Kasar Amurkan wannan kashedi.

Jahohin da Amurkar ta yi wa 'yan Kasar ta gargadin cewar su kiyayi kai ziyara a Najeriyar sun hada da Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Edo da kuma Jahar Rivers a yankin Neja Delta.

Sai kuma jahohin Aba da Imo dake kudu maso gabacin Najeriyar.

A arewacin Najeriya kuwa, jahohin da Amurka tace 'yan Kasar ta su kiyayi zuwa sun hada da jahar Filato, Bauchi da kuma Borno.

Amurka dai ta shawarci 'yan Kasar ta da cewa daga yanzu, su tabbatar da cewa sun nemi izini kafin su yi balaguro zuwa wasu sassan Najeriyar.

Karin bayani