BBC navigation

ICC ta bada sammacin kame Abduraheem Hussein na Sudan

An sabunta: 2 ga Maris, 2012 - An wallafa a 05:48 GMT
Shugaban Sudan Omar Al Bashir

Kotun manyan laifuka dake Hague na cajin ministan tsaron Sudan da aikata laifukan yaki

Kotun hukunta masu aikata miyagun laifuka ta kasa da kasa ta bayar da sammacin kame Ministan tsaro na kasar Sudan Abdur-Raheem Mohammad Hussein.

Kotun tace akwai kwararan hujjoji da ake da su na cajin Ministan da aikata laifukka 41 na cin zarafin bil-adama da laifukkan yaki da aka tafka a lokacin rikicin Darfur da aka yi a tsakanin shekara ta dubu biyu da uku zuwa da hudu.

Kotun wadda ke Hague dama ta riga ta bayar da sammacin kame Shugaban Kasar ta Sudan Omar Hassan al-Bashir, wanda ake caji da hada makarkashiyar kisan kiyashi.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.