Za a samu madaidacin ruwan sama bana a Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Hasashen yanayi na nuna cewar za a sami yabanya mai kyau a daminar bana a Najeriya

Hukumar da ke kula da hasashen yanayi a Najeriya ta yi hasashen cewa, za a sami madaidaicin ruwan sama a damunar bana.

A rahoton da ta fitar, hukumar ta kara da cewa, a wannan shekarar za a sami yabanya mai kyau a Kasar, musamman idan manoma su ka yi shuka a lokacin da ya kamata, tare da yin amfani da iri mai inganci, da kuma takin zamani.

Sai dai kuma a cewar hukumar hasashen yanayin, akwai yiwuwar manoman za su fuskanci kalubale daga fari da tsuntsaye jan-baki, masu cinye amfanin gona.