An yi jana'izar Chief Odumegwu-Ojukwu

Ojukwu
Image caption Gawar marigayi Chukwuemeka Odumegwu-Ojukwu kafin a binne shi

Dubban jama'a ne a Kudu maso gabashin Najeriya suka halarci jana'izar tsohon madugun 'yan tawayen Biafra Chukwuemeka Odumegwu-Ojukwu.

Wakilin BBC AbduSsalam Ibrahim Ahmad a mahaifar Kanal Ojukwu ta Nnewi, ya ce dubban magoya bayansa ne suka taru a kan tituna, wasu a kan katanga domin ganin yadda bikin ya gudana.

A watan Nuwamban da ya wuce ne Chief Ojukwun ya rasu a birnin London, yana mai shekaru 78.

Ikirarin da ya yi na kafa kasar Biafra a 1967 ya haifar da yakin basasa, inda fiye da mutane miliyan daya suka mutu.

Ya yi kaurin suna a fagen siyasar Najeriya inda ya yi takarar shugabancin kasa har sau biyu daga shekara ta 2000.

Kanal Ojukwu ya tafi gudun hijira bayan da Biafra suka mika wuya a 1970, sannan ya koma bayan sama da shekaru goma, sakamakon afuwar da aka yi masa.

Bayan afuwar da aka yi masa, an masa cikakkiyar jana'izar girmamawa irin ta soja, inda aka rinka kada gangar sojoji a gidansa da ke Nnewi, a jihar Anambra.

'Yan kabilar Igbo a wasu sassan Najeriyar ba su fita aiki ba, inda suka zauna a gida suna zaman makokin gwarzon nasu.

Karin bayani