An hana Red Cross shiga Baba Amr

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ayarin motocin kungiyar agaji ta Red Cross

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce an hana ayarin motocinta da ya isa birnin Homs na Syria izinin shiga unguwar Baba Amr inda ake matukar bukatar agaji.

Shugaban kwamitin Jakob Kellenberger, ya ce bai dace ba ko kadan a hana su shiga unguwar, inda mutane da dama ke matukar bukatar taimako.

'Yan gwagwarmaya a Syriar sun zargi hukumomin kasar da haddasa jinkirin da gangan, don dai su samu su boye shaidun abinda suka kira "mugayen laifufukan da suka aikata a Baba Amr din".

Tunda farko dai kungiyar ta Red Cross ta ce hukumomin Syria sun bata izinin shiga unguwar ta Baba Amr.

Kwamitin sulhu ya koka

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ce wajibi ne abayar da damar shiga da kayan agaji zuwa kasar ta Syria ba tare da bata lokaci ba.

Kasashen Rasha da China sun goyi bayan kudurin duk da adawar da suka nuna a baya, kan daukar mataki kan kasar ta Syria.

Wakilin BBC a Majalisar ya ce wannan ya haifar da kwarin gwiwar cewa, mai yiwuwa su goyi bayan yunkurin da ake yi na kawo karshen rikicin.

Kwamitin ya kuma bayyana rashin jin dadinsa kan yadda aka hana shugabar hukumar kula da ayyukan jinkai ta Majalaisar Valerie Amos, izinin shiga Syriar duk da cewa an nemi hakan ba sau dayaba-ba sau biyu ba.

Dakarun adawa sun janye

Mayakan yan adawa na Syria da ke gundumar Baba Amr da aka yiwa kawanyar tsawon makonni a birnin Homs, sun ce suna janyewa bisa dalilai dabarun yaki.

Wata sanarwa da aka fitar a wani shafi na Internet da sunan mayakan 'yan tawayen Syria a birnin Homs ta ce sun dauki matakin janyewa bisa dabaru irin na yaki.

Sanarwar wadda ta ce ta fito ne daga bataliyar Baba Amr - ta ce mayakan suna janyewa ne saboda la'akari da cewar har yanzu akwai farar hula a yankin.

Sanarwar ta kara da cewa mayakan basu da isassun makamai na kare fararen hullar.

Tun farko dai wani mai fafutuka da ke cikin birnin na Homs ya ce an yiwa birnin kawanya.

Karin bayani