Wasu mayakan ruwan Najeriya sun bace a Naija Delta

Wasu masu fafutika a Naija Delta Hakkin mallakar hoto b
Image caption Wasu masu fafutika a Naija Delta

A Nigeria rundunar tsaro ta hadin gwiwa watau JTF a yankin Niger Delta ta ce tana kan gudanar da bincike game da bacewar wasu sojojin ruwa su hudu.

Ta ce sojojin sun bace ne a lokacin da wasu yan bindiga da ba'a a san ko su wane ne ba suka kai ma su hari a garin Brass dake Jihar Bayelsa.

Kakakin rundunar tsaron ta JTF, Laftana kanal Timothy Antigha, ya ce sun fara shirin neman sojojin ruwan da suka bace, kuma sai sun kammala aikin kokarin ceto su ne za su yi karin haske a kan lamarin.

Rahotanni dai sun ce kungiyar nan mai fafutikar kwato yancin Niger Delta ta MEND ta yi ikirarin cewa ita ta kai hari.

Karin bayani