Kamfanin BP ya cimma 'yarjejeniyar biyan diyya

Tambarin kamfanin mai na BP Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Tambarin kamfanin mai na BP

Katafaren kamfanin mai na BP ya cimma yarjejeniyar biyan dala biliyan fiye da bakwai a matsayin diyya ga wasu mutane da ma harkokin kasuwanci da malalar mai a gabar tekun Mexico ta shafa shekaru biyu da suka gabata.

Yawancin wadanda za su samu diyyar dai masunta ne da suka rasa abin yi sakamakon malalar man.

Kamfanin na BP ya ce, biyan wannan diyya ba wai yana nufin cewa, ya dauki alhakin lamarin ba ne.

Har yanzu dai kamfanin na BP yana fuskantar shari'a daga gwamnatin Amurka da kuma wasu masu jari a kamfanin dangane da wannan batu.

Ma'aikatan kamfanin sha daya ne suka rasa rayikansu , kuma dimbin mai ya malala a gabar tekun na Mexico yayin da rijiyar man ta BP ta balle.

Karin bayani