Brazil ba ta shirin gasar kwallon kafa ta duniya - FIFA

Sepp Blatter, Shugaban hukumar FIFA Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption FIFA ta nuna damuwa game da shirye shiryen da Brazil ta ke yi na gasar kwallon kafa a shekara ta 2014

Babban Sakataren hukumar shirya gasar wasannin kwallon kafa ta duniya FIFA Jerome Valke, ya bayyana damuwar sa game da shirye-shiryen da Brazil ke yi na daukar nauyin gasar kwallon kafa ta shekara ta dubu biyu da goma sha-hudu.

Mr. Valke yace an taushe kafa wajen gina filayen wasanni da abubuwan sufuri da wuraren kwanan 'yan kallo.

Yace, hukumomin Kasar suna jan-jiki, akwai kuma bukatar abinda ya kira masu shirya wa gasar su tashi tsaye.

Babban jami'in na FIFA ya kara da cewa ga alama Brazil din ta fi damuwa ne da yadda za a yi ta laashe gasar, ba wai shirye-shiryen daukar nauyin gasar ba.