Za a bude bankuna domin nakasassu a Najeriya

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Za a bude rassan bankuna na musamman domin nakasassu a Najeriya

A Najeriya, Babban Bankin Kasar wato Central Bank of Nigeria, ya ce bankuna a Kasar za su bude rassa na musamman domin nakasassu.

Hakan a cewar Babban bankin zai bai wa nakasassun damar gudanar da harkokin banki a saukake.

Hakan kuwa ya biyo bayan kiraye-kirayen da nakasassun su ka yi, don su samu kulawa ta musamman a Bankunan.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Malam Sanusi Lamido Sanusi ne ya zayyana hakan a wata ganawa da ya yi da shuwagabannin nakasassu na Najeriya.

Wannan na zuwa ne a lokacin da Kasar ke ci gaba da sauye-sauye a harkar bankunan don ci gaban Kasar.

Nakasassun dai a Najeriya sun yi maraba da wannan sanarwa ta babban banki