An fara yunkurin rubuta sabon tsarin mulkin Masar

Hosni Mubarak Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hosni Mubarak

Wani zaman hadin gwiwa na majalisar dokokin Masar ya soma fasalin wani kwamiti da zai rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar da zai maye gurbin wanda shugabannin sojan kasar suka dakatar bayan tumbuke gwamnatin Hosni Mubarak.

Masu kishin Islama da suka samu rinjaye a zaben da aka yi a karshen bara sun ce, zasu zama gaba-gaba a kwamitin mai mambobi dari.

Masu aiko rahotanni sun ce, wannan zai kawo takun saka tsakanin masu kishin Islaman da sojan dake mulkin kasar, wadanda kuma suke cin gajiyar alfarma iri iri bisa kundin tsarin mulkin da ake aiki da shi yanzu haka.

Suma dai masu sassaucin ra'ayi suna na fargabar cewa, ba za su samu damar cewa komai ba a sabon kundin tsarin mulkin da za'a rubuta.

Karin bayani