Har yanzu baa kai agaji unguwar Baba Amr a Syria ba

Unguwar Baba Amr dake birnin Homs Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Unguwar Baba Amr dake birnin Homs

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce, ta fidda tsammanin shiga da kayan agaji cikin unguwar Baba Amr dake birnin Homs na Syria, wadda sojojin gwamnati suka kame, tun bayan da dakarun 'yan tawaye suka janye a ranar Alhamis din da ta gabata.

Tun farko hukumomin Syriar sun ba kungiyar ta Red Cross izinin shiga unguwar da kuma tura ayarin motocinta dauke da kayan agaji, daga Damascus zuwa birnin na Homs, amma har yanzu ba a kyale ayarin motocin su shiga unguwar ba saboda hukumomi sun ce akwai hatsari sosai.

Jami'an kungiyar ta Red Cross sun ce, zasu cigaba da tattaunawa da gwamnatin Syria dangane da wannan batu gobe Lahadi.

A halin da ake ciki kuma, kungiyar ta Red Cross ta mika wa jami'an Diplomasiyya a Damascus, gawarwakin 'yan jaridan nan 2 'yan kasashen waje da aka kashe a luguden wutar da aka yi a kan unguwar ta Baba Amr a makon jiya.

Karin bayani