'Yan bindiga sun kashe mutane hudu a Maiduguri

Wasu 'yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu 'yan sandan Najeriya

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno sun ce wasu 'yan bindiga sun hallaka kimanin mutane hudu da suka hada da wata mace da dan ta mai kimanin shekaru goma, a daren jiya.

An kashe mutanen ne dai a unguwanni daban daban da aka fi samun kai hare hare a tsakiyar birnin.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Borno ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Wannan dai shine karon farko da yan bindiga suka kaiwa mace hari a birnin na Maiduguri.

Wani dan kasuwa mazaunin unguwar zannari inda matar ke zaune, ya shaida wa BBC cewa bai gama fita daga jimamin kisan matar da danta na daren jiya ba, sai ya sake iske wani kisan da aka yiwa wani mai shagon sayar da waya a kasuwar shani dake tsakiyar birnin dazu da safe.

An dai samu salwantar rayukan jama'a da dama cikin irin jerin hare hare da kashe kashen dake faruwa a birnin Maiduguri da ma wasu sassan jihar a cikin shekaru biyun da suka gabata, kuma galibi 'ya'yan kungiyar nan ta Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati waljihad da aka fi sani da Boko Haram ne ke daukan alhakin kai hare-haren.

Karin bayani