Amurka za ta ci gaba da shari'a da kamfanin BP

Kamfanin mai na BP Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ma'aikatar Shari'ah ta Amurka za ta cigaba da karar kamfanin BP

Ma'aikatar sharia'a ta Amurka ta yi kashedin cewa za ta cigaba karar hamshakin kamfanin man nan na BP, duk kuwa da sasantawar da aka yi tsakanin kamfanin da dubban mutanen da malalar man ta yi wa illa a tekun Mexico a shekara ta 2010.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta bayar, ta ce ta na fatan yarjejeniyar da aka yi za ta tabbatar da biyan diyya cikin hanzari ga mutanen da abin ya shafa.

To amma ma'aikatar shari'ar ta ce za ta cigaba da neman kamfanin man na BP ya biya diyya ga lalata muhallin da ya yi da kuma saba wa dokoki.

Mutane goma sha daya ne su ka mutu, kuma miliyoyin gngunan mai sun malale a tekun na Mexico, a lokacin da wani bututun man ya fashe.

Karin bayani