Mutane da dama sun hallaka a Congo

Ta'adin da gobarar ta yi a Brazaville Hakkin mallakar hoto
Image caption Ta'adin da gobarar ta yi a Brazaville

Rahotanni daga jamhuriyar Congo na cewa, kimanin mutane dari biyu ne suka mutu sakamakon fashewar wasu abubuwa a wani barikin soja.

Karar fashewar abubuwan ta auku ne sakamakon gobara a wani rumbun makamai a Brazaville, babban birnin kasar.

Shugaban wata cibiyar kiwon lafiya a birnin ya ce, yana da wuya a tantance yawan wadanda suka mutu, saboda lamarin ya rutsa ne da mutane da dama yayin da suke cikin gidajensu.

Wakilin BBC ya ce har ma a birnin Kinshasa na jamhuriyar dimukradiyyar Congo mutane sun tsere daga gidajensu bayan fashewar abubuwan karon farko, kuma lamarin ya yi kaca-kace da tagogi da rufin gidaje.