Yan gudun hijirar Baba Amr sun fara samun kayan agaji

Gine-ginen da aka lalata a Baba Amr Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gine-ginen da aka lalata a Baba Amr

Kungiyar agaji ta Red Cross ta soma raba kayan agaji ga mutanen da suka tserewa hare-haren da ake kaiwa unguwar Bab Amr dake birnin Homs na Syria.

Sai dai kuma har yanzu ba baiwa kungiyar ta Red Cross damar unguwar ta Bab Amr ba saboda gwamnatin Syria ta ce, akwai mummunan hatsari saboda nakiyoyin dake binne.

Kayan agajin sun hada da abinci da kuma barguna don kare kansu daga matsanancin sanyin da ake yi.

Sai dai kungiyar ta Red Cross ta ce har yanzu tana fatan shiga cikin unguwar ta Baba Amr, kuma za su cigaba da tattaunawa da hukumomin Syria a yau ma a kan batun.

Yanzu haka dai akwai motocin kungiyar ta Red Cross su 7 makare da kayan agaji , suna jiran shiga cikin Unguwar ta Baba Amr tun ranar Jumaa.

Karin bayani