Jiragen kasa biyu sun yi taho-mu-gama a Poland

Jiragen kasa biyu sun yi taho-mu-gama Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hotunan gidan talabijin na Poland sun nuna yadda turagun jiragen su ka baude

Mutane a kalla goma sha-hudu aka bayar da labarin sun mutu, akwai kuma fiye da sittin da su ka samu raunuka a wani hadarin jiragen kasa biyu da su ka yi taho-mu-gama a Kudancin Poland.

Hotunan da gidan talabijin na Kasar ya nuna, sun yi nunin yadda taraggan jiragen su ka baude, daya a kan daya.

Wani wanda ya tsira da ransa ya bayyana irin yadda aka cilla mutane sama tamkar jikkuna a lokacin hadarin.

Masu aikin ceto su na kokarin kaiwa ga mutanen da aka rutsa da su a cikin jiragen.

Jami'an hukumar jiragen Kasa a Kasar Poland din sun ce jiragen biyu su na tafiya ne a kan layi daya.