Sin ta yi hasashen ci gaban tattalin arziki

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Piraminsitan kasar China, Wen Jiabao

An bude taron yan majalisar dokokin kasar China na shekara shekara, inda jawabin bude taron da Piraministan kasar Wen Jiabao ya yi, ya fi maida hankali kan tattalin arziki.

Ya yi hasashen samun ci gaban kasar da kashi 7 da digo 7 cikin dari, kasa da hasashen da aka yi a shekarun da suka gabata.

A yayinda China ke kokarin rage dogaronta da kayanda take fitarwa ketare, Mr Wen ya ce, a yanzu gwamnatin kasar za ta fi maida hankali kan inganta ciniki na cikin gida.

Piraministan ya ce sauya fasalin masanaantu tare da inganta su a gabashin kasar na wakana ne cikin gaggawa.

ya kara da cewa fadada birane ya zarta kashi hamsin cikin dari. Wannan sauyi ne mai tarihi ga yanayin rayuwar China.

Karin bayani