Matan Ghana sun fi na Biritaniya adana kudi

Mata da yaro
Image caption Mata suna zage damtse

Wani bincike da wasu bankuna da kungiyoyi masu zaman kansu suka gudanar ya nuna cewa sama da kashi casa'in cikin dari na mata a Ghana ne ke kokarin ware kudi kowane wata su ajiye don nan gaba.

Sun yin adashe ne ko adana kudade wata-wata ko rana-rana.

Suna adana kudadaden da suke samu ne ta fuskar kasuwanci da sauransu.

Sun zarta mata a kasar Britaniya, inda adadin masu tanadin ba su fi kashi hamsin da biyar a cikin dari ba.

Binciken ya kuma nuna cewa kashi casa'in cikin dari na mata a Ghana ne ke sha'awar shiga harkar kasuwanci da kansu, maimakon kashi arba'in cikin dari da ake da su a Burtaniya.

Karin bayani