Wasu 'yan bindiga sun hallaka mutane 27

haditha Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu shigar burtu a Iraqi sun hallaka mutane 27.

A Iraki, wasu 'yan bindiga sanye da kayan sojojin gwamnati, sun kai hari akan wasu 'yan sanda a garin Haditha na yammacin kasar.

Akalla mutane ashirin da bakwai sun hallaka, ciki har da maharan uku.

Rahotanni sun ce, 'yan bindigar sun sa uniform din jami'an tsaron cikin gida, sannan suka tuka motocin ma'aikatar cikin gidan zuwa wuraren bincike na kan hanya, a yankin Haditha, inda suka rika bindige jami'an tsaron da ke bakin aiki.

Wakiliyar BBC ta ce "wasu 'yan bindigar kuma sun kai hari a gidan wani Kanar din 'yan sanda da yayi ritaya, da kuma wani kyaftin. Sun hallaka masu gadinsu, sannan suka yi awon gaba da mutanen biyu kamin daga baya sun bindige su".

Wani kakakin 'yan sandan Iraki ya dora alhakin hare-haren akan kungiyar al Qaeda.