Nijer za ta gina kasuwa a Maradi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Kasar Nijar, Mahamadou Issoufou

A Ranar Litinin ne a jihar Maradin Jamhuriyar Nijar, shugaban kasar Alhaji Mahamadou Issoufou ya aza tubalin farko na ginin kasuwar dake da mahimmancin gaske ga garin na Maradi.

Kusan shekaru biyu kenan da al'ummar wannan gari ke ta kiraye-kiraye don ganin an gina wannan kasuwa a garin da yake iyaka da Najeriya ta bangaren jihar Katsina. Tun lokacin da gwamnatin tsohon shugaban kasar Mamadou Tandja ta rushe kasuwar da zummar gina wata; har aka hambarar da mulkinsa ba a gina kasuwar ba.

Jama'ar garin dai sun yi lale marhabbun da wannan yunkurin na gwamnatin Kasar.

Sai dai suna fatan kuma cewa Gwamnatin za ta duba batun hanyoyi a garin, abunda zai bawa 'yan kasuwar damar zurga-zurga don inganta harkokin kasuwanci a yankin wanda yake daya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwancin Nijar.

Karin bayani