Obama da Netanyahu sun tattauna shirin nukiliyar Iran

Barack Obama da Bejamin Netanyahu Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bakinsu ya daidaita

Shugaba Obama ya gana da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, a fadar White House, inda suka tattauna game da damuwar da suke da ita a kan Iran.

Amurka da Isra'ila na zargin Tehran da kokarin kera makaman nukilya, amma a baya sun sha ban ban game da matakan da ya kamata a dauka.

Shugaba Obama ya yi kira ga Isra'ila cewa kada ta hanzarta daukar matakin soji.

Su bi hanyar difilomasiya.

Yayin da Firaministan Isra'ila da shugaban Amurka suka zauna gefe da gefe suna kallon na'urorin daukar hoto, tattaunawar ta fi karfafa ne a kan yarjejeniya.

Shugaba Barak Obama dai shida Firaminista Netanyahu sun fi yarjewa amfani da diplomasiyya fiye da karfin soji wajen gano bakin zaren.

Ya ce na bar duk wani zabi, kuma manufofi na su ne na hana kasar Iran mallakar makaman nuclear.

“Na san cewa ni da Firaminista mun fi yarda da shawo kan wanann matsala ta hanyar diplomasiyya.

“Mun gano illolin amfani da karfin soji,kuma ina so in baku tabbacin cewar Mutanen Amurka da Isra'ila muna kan tuntubar juna.”

Firaministan Isra'ilar da ke ya dora hannaye a kan gwiwarsa, na sauraro yana gyada kai lokaci-lokaci.

A gare shi manyan kalaman sune amincewar da shugaba Obama yayi na cewar Isra'ila nada cikakken yancin ta dauki matakai na kashin kanta.

Lokacin da yake nasa jawabin a fadar White House Mista Netanyahun ya ce ya samu karfin gwiwa tunda Amurka ta fahimci yadda batun tsaro ke da muhimmanci ga kasar Isra'ila.

Isra'ila na da damar ata kare kanta daga kowace irin barazana a koyaushe, kuma idan aka zo ta fuskar harkar tsaron Isra'ila,

Isra'ila na da yancin da yanke shawara bisa radin kanta.

Lokaci ya yi da shugaba Obama zai gyada kansa domin nuna gamsuwa da amincewarsa.

Fadar White House na ganin cewar ya kamata a dakatar da kasar Iran daga mallakar makaman nuclear, yayin da Isra'ila na ganin ya fi alfanu shi ne kada a bar ta ta samu isasashen sinadarin yuranium da za ta iya hada bamabamai, sai dai a yanzu kam batun da ake shi ne na nuna hadin kai da goyon baya.

Karin bayani