Vladimir Putin zai koma Kremlin

murnar nasarar Putin Hakkin mallakar hoto AP
Image caption murnar nasarar Putin

Vladimir Putin da magoya bayan sa suna ci gaba da murnar nasarar da ya samu a zaben kasar Russia inda zai koma fadar shugaban kasar ta Kremlin.

Sakamako na baya bayan nan da aka samu bayan kammala kidaya kashi ukku cikin hudu na kuriunda aka kada ya nuna Mr Putin na kan gaba da kashi sittin da biyar cikin dari.

A lokacin da yake jawabi ga wani gangami a cikin dare, cikin hawaye Mr Putin ya bayyana godiyar sa ga abokan sa, inda ya ce nasarar da ya samu babu tantama a kai.

To sai dai kungiyar dake sa ido kan zaben kasar guda daya tilo, ta ce adadin sakamakon zaben bai yi daidai ba.

Karin bayani

Labaran BBC