Tsarin Federaliya a Libiya

Taron shugbannin gabashin Libiya Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Taron shugabannin gabashin Libiya

Shugabannin kabilu da kwamandojin dakarun sa-kai a birnin Benghazi dake gabashin Libiya, sun bayyana yankinsu mai arzikin man fetur a matsayin mai kwarya-kwayar cin gashin kai.

A cewarsu, an shafe shekara da shekaru ba a kula da yankin gabashin Libiyar da ake kira Cyrenaica.

Don haka a yanzu sun zama jaha a karkashin tsarin Federaliya.

Shugabannin har ila yau sun kafa wata majalisa da zata tafiyar da harkokin yankin.

Sai dai Majalisar rikon kwaryar Libiyar, wadda ta jagoranci kifar da gwamnatin Kanar Gaddafi daga Benghazi, ta nisanta kanta daga batun neman 'yancin yankin.

Karin bayani