Wutar data tashi a wajen hako gas ta mutu

chevron
Image caption Gobarar data tashi a gabar tekun Najeriya

Gobarar data shafe kwanaki 46 tana ci a wani wurin hako iskar gas a gabar tekun Najeriya, ta mutu da kanta.

Kamfanin hakar mai na Amirka, Chevron shine ya mallaki wurin, ya kuma ce wutar ta daina ci ne da kanta.

Masu rajin kare muhalli sun bukaci kamfanin Chevron din ya baiwa masunta a yankin diyya, saboda daina kama kifin da suka yi sakamakon gobarar, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu.

Al'ummar kauyen sun kuma ce, sun shiga fargaba akan irin illolin da iskar gas din zai yiwa muhallin.

Amma kuma kamfanin na Chevron ya ce gobarar bata janyo malalar mai ba.