Wasu jiga jigan masu satar shiga Kwamfutocin jama'a sun shiga hannu a Amurka

Tamburan hukkumar bincike ta Amurka -FBI Hakkin mallakar hoto FBI
Image caption Tamburan hukkumar bincike ta Amurka -FBI

Hukumomin tsaro a Amurka sun ce sun damke wasu jiga-jigan masu satar bayanan jama'a a Intanet da ake kira LulzSec.

Ana zarginsu da hannu wajen satar shiga adireshin intanet na manyan hukumomi ciki hadda hukumar CIA, da hukumar 'yan sanda Birtaniya da kuma kamfanoni kamarsu Sony da Mastercard da kuma Paypal.

Daya daga cikin wadanda aka kama ya dauki alkawarin bada hadin kai ga hukumomin Amurka don ya samu sassauci.

Wakilin BBC yace , wani mutumin da ake ganinsa a matsayin shugaban gungun masu satar bayanan, wato Lulzsec, yana fuskantar tuhumce tuhumce 12, ciki har da, hada baki wajen aikata zamba.

Karin bayani