Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya ta shiga birnin Homs

Birnin Homs Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An yi wa yankin kaca-kaca

Shugabar ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya, Valerie Amos, ta kai ziyara gundumar Baba Amr da ke birnin Homs na Syria, inda aka tafka ta'asa.

Ta shafe kusan mintuna 45 tare da mambobin kungiyar agaji ta Syrian Red Crescent, inda ta yi nazarin irin abubuwan da al'ummar yankin ke bukata, wadanda suka dade sojojin gwamnati na yi musu luguden wuta.

Kakakin Red Crescent din ya ce yawancin jama'ar Baba Amr sun yi kaura.

Can kuma a Amurka, Sakataren tsaron kasar Leon, Panetta, ya jaddada cewa dakarun Amurka ba za su jagoranci kawar da shugaba Assad ba.

Yace, “Ba wai muna jan kafa ba ne.

“Gwamnatinmu ta jagoranci yaki a Iraki, da Afghanistan da Libya da kuma ta'adanci baki daya.

A yanzu muna aiki da kawayenmu a kan yadda za a hada gwiwa.

Karin bayani