Sojan Birtaniya 6 sun hallaka a Afghanistan

Sojan Birtaniya a Afghanistan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sojan Birtaniya a Afghanistan

An kashe sojojin Birtaniya shida sakamakon fashewar wani bam a kudancin Afghanistan.

Mutuwarsu ta kawo adadin sojojin Birtaniya da aka kashe a Afghanistan ya kai fiye da dari hudu.

Dakarun Birtaniya sun dauko gawarwakin sojojin da kuma motarsu da ta yi kaca kaca a lamarin daya auku lokacin suna sintiri.

Wani kwamandan sojojin Afghanistan, Manjo Ram Ali, ya ce 'yan Taliban ne suka dasa bam din.

Ya ce, “Kamar yadda kuka gani, 'yan Taliban ne suka dasa nakiyar.

“A lokacin da sojojin Birtaniya suke wucewa a kan hanya ne nakiyar ta fashe.

“Mun shafe daren jiya muna taimakawa wajen kwashe sojojin da suka tsira da ransu da kuma motarsu da ta lalace.”

Tuni dai Pirayi Ministan Birtaniya David Cameron ya jinjina wa sojojin, inda ya ce sun sadaukar da kai wajen kishin kasa.

Karin bayani