An kashe Turawan nan biyu da aka yi garkuwa da su a Kebbi a bara

David Cameron Hakkin mallakar hoto cameron
Image caption David Cameron

Firaministan Birtaniya, David Cameron, ya bada sanarwar cewa, wani yunkuri ya ci tura na kubutar da wani injiniya dan Birtaniya da abokin aikinsa dan kasar Italiya da aka sace a Nijeriya, kuma dukkan mutanen biyu sun rasu.

Mr Cameron ya ce bayanan farko na nuna cewa, wadanda suka sace Chris McManus da Franco Lamolinara su ne suka kashe su kafin a kubutar da su.

Wani mazaunin birnin Sokoto, inda lamarin ya faru ya ba da karin haske kan musayar wutar da aka yi.

An ba da rahoton kasha biyu daga cikin wadanda suka sace mutanen, aka kuma kama ransu da ransu.

Mutane biyar ke nan suka rasa rayukansu a harin neman kwato sun, wato wadanda aka sacen da kuma ukku daga cikin wadanda suka sace sun.

A cikin watan Mayun bara ne aka sace su a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Nijeriya.

Karin bayani