China zata bude Kamfanin Suga a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption mataimakin shugaban kasar China, X1 Jinping

Kasar China ta bayyana anniyarta ta kafa wani babban kamfanin sukari a kasar Nijar, wanda zai samar da aiyukanyi dama sukarin da kasar ke shigowa dashi.

Ko da yake izuwa yanzu Kasar ta China ba ta yi wani karin haske game da lokacin da za ta fara aikin ba, amma Kamfanin zai samarda tan dubu dari na sukari.

Haka kuma Kamfanin zai samar da aiyukanyi dubu goma matswar ya fara aiki.

Kamfanin dai zaa yishi ne a garin Doso mai nisan kilomita dari da arbain daga Yemai babban birnin Kasar.

Jamhuriyyar Nijar dai na yin noma rake mai tarun yawa, amma kuma ba ta mallaki kamfanin sukari ba, abunda ke sa ta shigo da sukarin da take amfani dashi daga kasashen waje.

Karin bayani