Sakin aure ya yawaita a Kasar Hausa

Wasu mata na gudanar da aiki Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yau ake gudanar da bukukuwan zagayowar ranar mata ta duniya

A yayinda ake bukin tuna ranar mata ta duniya a yau, inda ake sa ran gudanar da bukukuwa fiye da dubu don zagayowar ranar, yawan sakin aure na karuwa a Kasar Hausa.

Yawan sake-saken mata na daga abinda masu lura da al'amura ke cewa na jefa matan cikin rayuwa mara kyau.

Sau da yawa dai akan bar matan da aka saki da yara, mazan kuwa na shiga sharafin gabansu; wasu ma sukan sake wani auren.

Hakan dai na sa matan daukar wahalhalun yaran da aka bar musu, kama daga abubuwan da su ka shafi abinci da tufafi da kuma kula da lafiya, inda kuma a mafi yawancin lokuta su matan basu da wata madafa.

Shugabar Muryar Zawarawa da Marayu a Jihar Kano dake arewacin Najeriya, Hajiya Atine Abdullahi ta shaidawa BBC cewa rashin tallafi ga zawarawan na jefa su cikin wani halin ha'ulai.

Hakan na tilastawa wasu matan yin ayyukan kaskanci, wasu kuwa na shiga halin masha'a don daukar dawainiyar yaran da aka bar masu.

Karin bayani