Wani minista ya sauya sheka a Syria

Mataimakin ministan mai a Syria, Abdo Hussam Eddin yace ya sauya sheka daga bangaren gwamnati domin ya shiga cikin abun da kira juyin juya hali na jama'ar kasar.

Mr Hussam shine babban jamii da zai sauya sheka tun da aka fara boren da akeyiwa shugaba Al assad a shekerar data gabata.

A cikin wani sako bidiyo Mr Hussam yace yana sa ran mahukuntan kasar zasu mayar da martani ta hanyar kona masa gida da kuma neman iyalinsa

Sai dai wakili na musaman na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar kasashen larabawa, Kofi Anan, yayi gargadin cewa daukar matakin soji daga wurin kasashen duniya zai sa alamura su kara tabbabarewa.