Yansandan Burtaniya na farautar Samantha

Image caption Yansandan kwantarda tarzoma a Burtaniya

Yansandan Burtaniya da Kenya na ci gaba da neman tsohuwar matar wanda ake zargin cewa shi ne ya kai mummunan harin bom na kunar-bakin wake a London, a ranar Bakwai ga watan Yulin shekara ta 2005.

An yi amanna cewa tun a bara ne matar mai suna Samantha Lewthwaite, 'yar shekaru Ashirin da Takwas, ta shiga kasar Kenya, kuma yan sanda na zargin cewa ta kulla makircin kai wasu hare-haren na'addanci.

Tuni dai yan sanda suka cafke wani dan kasar Birtaniya mai suna Jamaine Grant, wanda a halin yanzu yake zaman wakafi a gidan yarin kasar ta Kenya bisa zarginsa da shirya kai harin bom

ana dai zargin cewa matar tana kokarin kitsa kai wani harin bom a wani otel dake Kenya. Tun daga watan Disambar shekarar da ta wuce take wasan buya dajamian tsaro

Karin bayani