Mata sun yi kiraye-kiraye a wannan rana ta mata ta duniya

Mata a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Matsalolin mata suna da yawa

A wannan rana ta mata ta duniya, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana, wasu kungiyoyin kare hakkokin mata da yara a Naijeriya sun nemi a kafa bankin tallafawa harkokin ilimi kyauta ga yara marasa galihu a makarantun kasar.

Kungiyar fadakar da mata ta "Arise women" tare da Save Nigeria Group ne suka bayyana hakan a lokacin wani jerin gwano da iyaye mata da yara 'yan makaranta suka gudanar a Lagos.

Yara matan sun yi gangamin a ci gaba da bikin wannan rana ta mata ta duniya a yau.

A bana a Jamhuriyar Nijar kamar sauran kasashe na duniya na bikin zagayowar ranar mata ta duniya .A wannan shekarara dai matan Nijar din na bikin ne cikin murnar ci gaban da suke samu a kowane fanni na rayuwa.

Ginshikin wannan ci gaba shi ne illimantar da 'ya'ya mata da iyaye ke yi sabanin lokutan baya da ake kalon ilmi tamkar wata hanyar lalacewa ce ga 'ya'ya matan .