Kasar Girka ta yi na'am da yarjejeniyar Turai kan bashin

Evangelos Venizelos, Ministan Kudi na Girka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Evangelos Venizelos, Ministan Kudi na Girka

Ministan kudinkasar Girka , Evangelos Venizelos ya ce irin rawar ganin da kamfanoni masu zaman kansu suka taka wajen canza takardun bashin gwamnatin kasar Girka na dubban miliyoyin euro, ya yi matukar zarta yadda aka za ta.

Ya shaidawa majalisar dokokin kasar cewa a karjkashin yarjejeniyar, za a yafe ma Girka bahsin sama da euro biliyan dari, matakin da ya ce yana cike da tarihi.

Ya kuma ce hakan zai taimaka ma kasar ta matsa gaba; Ya ce, ba zamu iya janyo masu saka jari a kasarmu ba, da bada kariya ga bunkasar tatatlin arziki da kirkiro guraben aiki, ba tare da tsarin banki mai goyon bayan saka-jari ba.

Tun da farko gwamnati ta ce sama da kashi tamanin da biyar cikin dari na masu bin ta bashi sun amince su tafka asara mai yawan gaske.

Karin bayani